Idris Ahmed, shi ne akanta janar na Najeriya, cikin wani jawabi da ya gabatar a Abuja, babban birnin kasar, ya ce, sanarwar da asusun ba da lamini na IMF ya fitar a kwanan nan cewa Najeriya ce ke kan gaba ta fuskan karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, alamu ne dake nuna cewa tattalin arzikin kasar na samun bunkasuwa.
IMF, ta sanar a cikin rahotonta na watan Oktoba game da hasashen ci gaban tattalin arzki, inda ta nuna cewa, Najeriya ce ke sahun gaba ta fuskar karfin tattalin arziki a Afrika inda ta sha gaban kasashen Afrika ta kudu da Masar, duk kuwa da matsayin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, wanda ba ta taba ganin kamarsa ba cikin shekaru 29.
Najeriya ta fada cikin halin matsin tattalin arziki ne a ranar 31 ga watan Augusta, a lokacin da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar da alkaluman tattalin arziki na GDP, dake nuna cewa tattalin arzikin kasar ya ragu da kashi 2 da digo 6 a watanni 4 na biyu na wannan shekara, bayan da ya ragu da digo 4 a watannin hudun farko na shekarar nan.
Masana harkokin kudade sun bayyana halin tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta da cewa shi ne mafi muni da kasar ta taba shiga, yayin da wasu ke ganin za'a iya shafe shekaru a kalla 3 kafin tattalin arzikin kasar ya koma hayyacinsa. (Ahmad Fagam)