Gwamnatin kasar Nijar a yayin wani taron ministoci ta cimma wasu jerin kudurori dake shafar bude kasuwar wutar lantarki tare da tsaida matakan ba da lasisin shigo da fitar da wutar lantarki, a cewar wata majiyar hukumomin kasar a ranar Asabar a birnin Yamai. Kudurin farko na tsaida musamman ma matakan shiga ga kamfanoni ga aikin layin sufurin wutar lantarki a dukkan fadin kasar, tare da biyan kudin hakkin samun dama, in ji sanarwar gwamnatin Nijar. (Maman Ada)