in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Suarez ya ja damara yayin da Uruguay ta yi kunnen doki da Colombiya
2016-10-12 16:44:17 cri
Luis Suarez ya zara kwallonsa ta 3 cikin wasanni 6 a yayin da Uruguay ta yi kunnen doki da Colombia da ci 2-2 a wasan share fagen shiga gasar kwallon kafa ta duniya.

Abel Aguilar shine ke kan gaba wajen zarawa Colombiyan kwallo cikin mintoci 15 da fara wasan, bayan da ya sha gaban Luis Muriel kafin ya zagaye Christian Rodriguez kuma ya kasance a kan gaba daga dandazon 'yan kallo.

Daga bisani Suarez ya sa Uruguay a gaba bayan da ya kai wani zazzafan hari daga wata kusurwa mai sarkakiya. To sai sai Yerry Mina ya ceto mai masaukin bakin a lokacin da buge kwallon da ka a Juan Cuadrado.

Suarez ya shedawa gidan talabijin na ESPN cewa, "da farko muna jin cewar kamar zamu yi nasara a wannan wasan, amma abin takaici sai gashi mun tashi kunnen doki".

A halin yanzu Suarez ya zarawa Barcelona kwallaye 3, baya ga taimako da ya samar wajen zara kwallaye a kalla sau 6 cikin wasan da aka gudanar a gasar share fagen shiga gasar cin kofin duniya.

Germany ta doke Arewacin Ireland da ci 2-0 a gasar wasannin share fagen shiga kwallon kafa ta duniya

Joachim Loew ne ya tabbatar da nasarar kungiyar wasan ta kasar Jamus a karo na 3 daga cikin illahirin wasannin da suka buga, wanda aka tabbatar da fidda kungiyar wasa ta arewacin Ireland da ci 2-0 baya ga namijin kokarin da Julian Draxler da Sami Khedira suka nuna a gasar share fagen shiga kwallon kafa ta duniya ta FIFA a 2018 a rukunin C.

Wannan nasarar ta tabbatar da yunkurin da suke yi 100 bisa 100, na neman kafa tarihi, bayan kwallayen farko daga Wolfsburg's Draxler da Juventus' Khedira suka yi nasarar zarawa, wanda ya baiwa Jamus nasarar tsallakewa bayan data doke arewacin Ireland, wadan da sune na farko da aka fara fitarwa daga shiga wasar ta FIFA a 2018.

Bisa wannan sakamako, Loew ya zara kwallaye kimanin 94 ga kungiyar wasan ta kasar Jamus. Yanzu dai, Jamus tana kan gaba da maki 2 a rukunin C, sai Azerbaijan, da arewacin Ireland, Norway, Czech Republic da kuma San Marino dake bi mata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China