in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sifaniya ta doke Albania a kokarin ta na samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2018
2016-10-12 16:43:04 cri
Kungiyar kwallon kafar kasar Sifaniya ta doke ta Albenia da ci 2 da nema, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na hukumar FIFA, wanda kasar Rasha za ra karbi bakunci a shekarar 2018.

'Yan wasan kasar Diego Costa da Nolitio ne suka ciwa Sifaniyar kwallayen biyu, a wasan da kasashen suka buga a filin wasa na Loro Borici dake birnin Shkoder na kasar ta Albania.

Kungiyar kasar ta Sifaniya dai ita ce ta mamaye maki kusan 70 na rike kwallo a wasan na karshen mako, kana ta samu nasarar lashe maki uku baki daya, a wani mataki da ake kallo a matsayin Laraba ta gari, ga sabon kocin kungiyar Julen Lopetegui, wanda wasan sa na 3 ke nan da kungiyar ta Sifaniya.

Matsalar da Sifaniyar ta fuskanta a wasan dai ita ce ta rauni da dan wasan ta Ramos ya ji, mintuna 10 gabanin tashi daga wasan.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China