Ibok-Ete Ibas, shi ne babban hafsan sojojin ruwan kasar, ya tabbatar da hakan a garin Onne na jihar Rivers dake kudancin kasar, ya kara da cewa, sojojin ruwan kasar sun taka rawa wajen dakile hare hare ba kakkautawa da tsageru ke kaddamarwa kan manyan jiragen ruwa a tekunan kasar.
Ibas , tura jiragen ruwan yaki masu yawa da gwamnati ta yi zuwa yankin, ya taimaka wajen samun wannan nasara.
A cewarsa, dakarun sojin ruwan kasar na ci gaba da sintiri domin dakile aniyar ba ta garin dake fashin jiragen ruwa a tekunan kasar, musamman a yankin da ake jigilar danyen man kasar.
Ibas ya ce, aikin da jami'an nasu ke yi, zai taimakawa manyan jiragen ruwan 'yan kasuwa su samu damar gudanar da zirga zirgarsu ba tare da fuskantar wata matsala ba, da kuma kare arzikin mai da iskar gas na kasar domin inganta samar da kudaden shigar kasar. (Ahmad Fagam)