in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukan Najeriya sunce shata kan iyakar kasar da Nijer ba zai haifar da sabani ba
2016-10-22 12:29:39 cri
Jami'an gwamnatin Najeriya sun ce yunkurin da kasar ke yi na shata kan iyakoki tsakaninta da jamhuriyar Nijer ba zai haifar da rashin jituwa tsakanin al'ummomin kasashen biyu ba.

Muhammad Bose, shi ne ke shugabantar hukumar kula da kan iyakokin kasar, ya ce gwamnatin Najeriyar ta yanke shawarar shata kan iyakokin kasar ne da makwabciyarta domin karfafa hadin kai, da zaman lafiya, da raya al'adu, da kuma bunkasa ci gaban tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

A cewarsa, aikin shata kan iyakokin da ake shirin gudanarwa, da ma tuni mahukuntan kasashen biyu suka cimma matsaya kansa, wanda ake sa ran aiwatarwa da nufin samar da ababan more rayuwa, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al'ummomin dake zaune a garuruwan kan iyakokin kasashen biyu.

Al'ummomin kasashen Najeriya da Nijer dake zaune a yankunan kan iyakokin kasashen biyu sun jima suna zaune lafiya da junansu, baya ga musayar al'adu, da addini da cinikayya da kyakkyawar mu'amala dake wanzuwa tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Jami'an gwamnatin sun ce, tun bayan lokacin da Turawan mulkin mallaka suka kirkiro tsarin shata kan iyakoki na kasashen Afrika, ba'a aiwatar da shata kan iyakokin kasashen biyu ba, amma duk da haka, matakin shata kan iyakokin na Najeriya da Nijer, ba zai taba raba kan jama'ar kasashen biyu ba sai dai ma a samu karin fahimtar juna a tsakanin su. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China