in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka: An fara bincike game da batun harin da jirgin sama maras matuki ya kaiwa sojojin Somaliya
2016-10-13 10:30:51 cri
A jiya Laraba ne, jakadan Amurka a Somaliya, Stephen Schwartz ya ba da sanarwa cewa, gwamnatin Amurka ta fara yin bincike game da harin jirgin sama maras matuki na Amurka ya kai a kan sojojin Somaliya a karshen watan Satumban bana a yankin tsakiyar kasar Somaliya.

Gwamnatin wucin gadin Galmudug (IGA) ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, ta yi bakin ciki game da yadda sojojin Amurka ke nuna karfin tuwo, inda ta bukaci gwamnatin Amurka da ta gudanar da bincike kan wannan batu. A sa'i daya kuma, sanarwar ta zargi gwamnatin yankin Puntland na Somaliya da mika sakon asiri da ba shi ne ba ga sojojin Amurka. Sojojin Amurka sun yi amfani da wannan sako ne, inda suke zaton cewa, sun kai hari ne kan kungiyar Al Shabaab mai tsattsauran ra'ayi ta Somaliya. Sanarwar ta ce, watakila da gangan gwamnatin Puntland ta yi haka.

A ranar 28 ga watan Satumba ne, wani jirgin saman Amurka maras matuki ya kai hari kan wani sansanin soja na Galmudug, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 22, yayin da wasu sojoji 16 kuma suka ji rauni. Lamarin ya haddasa zanga-zanga a yankin.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China