Jam'iyyar ta yi wannan kiran ne yayin da kasar ta ke bikin tunawa da masu aikin hakar ma'adinai 34 da 'yan sanda suka harbe shekaru 4 da suka gabata. Al'amari mafi muni da ya faru a bangaren hakar ma'adinan kasar tun bayan zamanin nuna wariyar launin fata.
Kakakin jam'iyyar ANC Zizi Kodwa ya ce, koyi da abubuwan da suka faru, za su taimakawa kasar wajen ganin ba ta sake faduwa cikin irin wannan al'amari ba. Ya ce wajibi ne hukumomi su rika kare 'yancin ma'aikata, ciki har da samar musu da yanayin aiki mai kyau, kuma wannan shi ne musabbin tashin hankalin na Marikana.
A saboda haka, jam'iyyar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin aiki tare, don ganin an dawo da zaman lafiya a wannan yanki.
Mahukuntan kasar Afirka ta kudun dai sun yi alkawarin magance matsalolin da ke addabar bangaren jin dadin jama'a da na tattalin arzikin kasar.
A ranar 16 ga watan Agustan shekarar 2013 wato shekaru 4 da suka gabata ne, aka yi arangama tsakanin masu aikin hakar ma'adinai da 'yan sanda a mahakar Lonmin da ke Marikana a lardin North West.(Ibrahim)