in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Afirka ta kudu za ta gabatar da korafinta a yayin babban taron MDD
2016-09-18 13:01:15 cri
Rahotanni daga kasar Afirka ta kudu na cewa, kasar za ta ci gaba da bayyana damuwarta game da karfin hukumomi game da tafiyar da harkokin mulki a duniya, ciki har da MDD, musamman kwamitin tsaron majalisar.

Fadar shugaban kasar ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, yayin da shugaba Jacob Zuma ya isa birnin New York na kasar Amurka don halartar babban taron MDD karo na 71. Muhawarar majalisar wata dama ce ga kasashe mambobinta wajen yin bitar tsiran majalisar, ana kuma sa ran kasashe mambobi za su yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a inganta tasirin majalisar ta yadda za ta rika gudanar da ayyukanta bisa tsarin demokiradiya, gaskiya da kuma adalci.

Ana kuma sa ran za a tattauna batun yiwa MDD kwaskwarima, ciki har da farfado da babban taron na MDD, inganta ayyukan hukumar kula da tattalin arziki da jin dadin jama'a, da kuma yiwa kwamitin tsaron majalisar gyaran fuska. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China