in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD bai zartas da daftarin kudurori biyu game da Syria ba
2016-10-09 09:54:11 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya jefa kuri'a kan wani daftarin kudurin da kasashen Faransa da Spaniya suka gabatar da wani daban da kasar Rasha ta gabatar kan batun Syria a jiya Asabar, amma bai zartas da su ba.

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya ba da jawabi bayan taron cewa, dole ne matakan da kwamitin sulhu na MDD ya dauka kan batun Syria su taka rawa wajen sassauta halin da kasar ke ciki, da ingiza tsagaita bude wuta a tsakanin bangarori daban daban, tare da ba da taimako ga aikin jin kai da MDD ke gudanar domin ceton mutane. Ban da haka kuma, ya kamata su ba da taimako wajen yaki da kungiyar IS da kuma sauran kungiyoyin ta'addanci, da kuma tsara shirin yunkurin siyasa da bangarori daban daban za su amince a karkashin aikin shiga tsakani da MDD ke yi.

Bugu da kari, Mr. Liu ya ce, daftarin kudurin da kasashen Faransa da Spaniya suka tsara ya shafi ayyukan ingiza tsagaita bude wuta da daidaita batun ta hanyar siyasa da kyautata yanayin jin kai da kara yaki da ta'addanci, amma sun kasa girmama ikon mulkin kasar Syria da cikakken yankin kasa da kuma sauransu. Shi ya sa, kasar Sin ta jefa kuri'ar kin amincewa da shi.

Ya kuma kara da cewa, daftarin kudurin da kasar Rasha ta gabatar ya shafi ayyukan tsagaita bude wuta da ceton jin kai da yaki da ta'addanci da yin shawarwarin siyasa, kuma ya girmama ikon mulki da cikakken yankin kasar Syria, kasar Sin ta nuna goyon baya gare shi, kuma ta yi nadama sabo da ba a zartas da shi ba.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China