Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan a lokacin taron manema labarai, ya ce hare-haren da mayakan Boko Haram suke kaiwa kan fararen hula, su ne suka kara bukatar kayan agaji a yankin da tun farko ya ke fama da tarin matsaloli.
Ya ce, da farko shirin na WFP ya taimakawa mutane miliyan 1 da ke yankin, amma duk da haka shirin ya yana kara agajin da ya ke bayar wa, saboda karuwar mutane da suke barin muhallansu, sannan kuma yanzu ana iya shiga wasu yankunan kasar ta Najeriya ba tare da wata matsala.(Ibrahim)