in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun musamman ta Afrika ta yanke wa tsohon shugaban kasar Chadi hukuncin daurin rai da rai
2016-05-31 11:18:12 cri

A jiya Litinin ne, kotun musamman ta Afrika dake birnin Darkar, babban birnin kasar Senegal ta yankewa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre hukuncin daurin rai da rai bisa zarginsa da aikata laifuffukan cin zarafin bil Adam da tada yake-yake da sauransu.

Tun a ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 2015 ne kotun musamman ta Afrika dake karkashin jagorancin kungiyar AU ta fara saurarron karar da aka shigar kan Hissene Habre.

Sai dai an sha dakatar da sauraron karar, sabo da Hissene Habre ya ki amincewa da matsayin wannan kotu.

Hissene Habre ya hau karagar mulkin kasar Chadi ne daga watan Yuni na shekarar 1982 ta hanyar yin juyin mulki, a watan Disamba na shekarar 1990, shugaban kasar Chadi na yanzu Idriss Deby ya hambarar da shi daga karagar mulki, daga bisani, ya gudu zuwa kasar Senegal. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China