in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ta halarci bikin rantsar da shugaban kasar Chadi
2016-08-10 10:06:42 cri

A ranar Litinin 8 ga watan nan ne wakiliyar musamman ta shugaban kasar Sin, kuma ministar shari'ar kasar Sin Madam Wu Aiying, ta halarci bikin rantsar da shugaban kasar Chadi Idriss Deby, wanda ya yi tazarce da mukamin sa, bikin da ya gudana a birnin N'Djamena fadar mulkin Chadi. Madam Wu ta kuma gana da shugaba Deby a jiya Talata 9 ga wata.

Yayin ganawar ta su, madam Wu Aiying ta ce Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasar Chadi ta fuskar zurfafa amincewar juna a fannin siyasa, da habaka hadin kai, da fadada mu'ammala tsakanin al'ummomi, tare da ciyar da dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci zuwa gaba.

A nasa bangare kuwa, shugaba Deby ya darajanta sabbin tunani da matakan da shugaba Xi Jinping ya gabatar game da inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika. Ya ce sakamako mai armashi da aka samu bisa wadannan tunani, da matakai, ya samu amincewa da karbuwa daga shugabannin kasashen Afrika baki daya. Deby ya ce, Chadi ta dauki kasar Sin a matsayin sahihiyar abokiya, yana kuma fatan kara habaka da inganta dangantakar sada zumunci tsakanin kasashen biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China