Kobler ya yi shawarwari da mambobin gwamnatin a birnin Tripoli a wannan rana, sannan a yayin taron manema labaru da aka shirya cikin hadin gwiwa tsakaninsa da mataimakin firaministan kasar Libya Ahmed Maiteeq, Kobler ya ce, yanzu, abun da ya fi kawo kalubale a kasar Libya shi ne kungiyar IS da sauran kungiyoyin ta'addanci dake ci gaba da habaka, kuma yanayin tsaro na kara tabarbarewa, sai dai gwamnatin hadin kan al'umma ya samu izni, tare kuma da karbar ayyukan kulawa da hukumomin gwamnati daban daban, za a iya warware matsalolin.
Martin ya ce, majalisar wakilan jama'ar kasar sun danka iznin ga gwamnatin hadin kan al'umma, wannan zai bai wa gwamnatin iko na halal wajen gudanar da ayyuka, ta yadda zai ba da amfani ga tabbatar da mika mulki cikin ruwan sanyi.(Bako)