in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An kori wasu jami'an kwastam daga aiki
2016-10-17 10:38:36 cri
Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa, an sallami wasu kananan jami'an hukumar kwastam su 17 daga aikin su, bisa aikata laifuka daban daban da suka hada da shan miyagun kwayoyi, da amfani da takardun bogi, da aikata sata, ko kauracewa wuraren ayyukan su babu dalili.

Kakakin hukumar ta kwastam a Najeriya Wale Adeniyi ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafin ta. Sanarwar ta kara da cewa an sallami ma'aikatan ne tsakanin watan Janairu da na Satumbar wannan shekara da muke ciki.

Mr. Adeniyi ya ce an riga an kammala bincike game da sauran manyan jami'an hukumar da suka aikata laifuka daban daban, kuma nan gaba kadan za a hukunta wadanda aka tabbatar sun karya dokokin ayyukan su. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China