in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Najeriya ya mika takardar nadi ga shugaban kasar
2016-10-19 08:55:45 cri

A jiya Laraba ne sabon jakadan kasar Sin a Najeriya mista Zhou Pingjian, ya mika takardar kama aikin sa ga shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar.

Jakada Zhou ya bayyana cewa, a matsayinsa na sabon jakadan Sin a Najeriya, zai hada kai tare da bangaren Najeriya, don tabbatar da nasarorin da aka cimma, a yayin taron kolin Johnnesburg na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma ziyarar shugaba Buhari a Sin a watan Aflilun bana, da nufin ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu gaba, kana da taka rawa wajen samar da gajiya ga jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangaren, shugaba Buhari ya jaddada cewa, yana maraba da kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Najeriya, domin samar da guraban aikin yi ga kasarsa, tare kuma da inganta masana'antu, da tattalin arzikin kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China