in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shawarci Najeriya da ta bullo da kyawawan dabarun bunkasa tattalin arziki
2016-10-15 12:15:56 cri
Wani kwararre a harkokin kudi mazaunin Legas, Bismarck Rewane, ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta gaggauta bullo da sahihan dabaru wadanda za su tallafawa kasar farfadowar daga halin komadar tattalin arziki da take fuskanta.

Rewane, wanda shi ne babban jami'i a kamfanin harkokin kudi na Derivatives Ltd, ya bayyana hakan ne a birnin Legas, ya ce matukar Najeriya ta yi amfani da matakan farfado da tattalin arzikin wadanda suka dace, to al'amurra za su iya komawa daidai kafin nan da shekarar 2018.

Ya ce, "ba zai wuce watanni 18 ba kasar za ta fita da halin durkushewar tattalin arzikin, kuma za'a fara ganin alamun farfadowa tun a shekarar 2017 matukar aka yi amfani da dabaru mafiya dacewa."

A cewarsa, akwai bukatar daukar matakan gaggawa, da yin gaskiya da jajurcewa matukar ana bukatar shawo kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta fada.

Ya kara da cewe, "idan kasar ta gaza daukar matakan a daidai wannan lokaci, matsalar za ta iya shafar kowa."

Rewane ya bukaci a kara hanyoyin ba da rance, sannan a sassauta sharrudan da bankunan kasar ke gindayawa wajen bada rancen kudade ga bangarorin da suka cancanta.

Masanin tattalin arzikin ya danganta matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta da rashin aiwatar da dabarun yadda ya kamata, da rashin kyakkyawan tsari game da sha'anin hada hada a cikin gida da kasashen ketare. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China