in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron AU kan tsaron teku da cigaba a Afrika ya cimma wani kundi na Lome
2016-10-16 13:10:13 cri
Shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar tarayyar Afrika (AU) sun cimma wani kundi kan tsaron teku da cigaba a Afrika, a yayin wani zaman taro a ranar Asabar a birnin Lome,.

Makasudin wannan kundin doka, da shugabanni da gwamnatocin AU suka rattaba hannu kansa shi ne na yin rigakafi da murkushe manyan laifuffuka na cikin gida da na kasa da kasa musammun ma ta'addanci, fashin taku, sata da makamai a kan jiragen ruwa, fataucin miyagun kwayoyi, satar shiga sauran kasashe , fataucin mutane, da kamun kifi ba bisa doka ba da sauransu.

Kundin ya jaddada muhimmancin kiyaye muhalli gaba daya da muhallin ruwa, musammun ma a yankin kasashen dake bakin ruwa da tsibirai, har ma da bunkasa da karfafa dangantaka a fannonin fadakar da jama'a kan harkokin teku, rigakafin abubuwa na ba zata da kuma yaki da 'yan fashin taku.

Haka kuma zai taimaka wajen kafa hukumomi a cikin gida, shiyya da ma yankin nahiyar da suka dace da tabbatar aiwatar da nagartattun manufofi da suka cancanci bunkasa tsaron teku.

A cewar wannan kundin, kowace kasar dake ciki ta dauki niyyar cigaba da kokarinta ta hanyar daukar matakan da suka dace domin samar da ayyukan yi, rage talauci da kawar da kangin talauci, bada kwarin gwiwa wajen fadakar da jama'a kan batutuwan teku ta yadda za a kafa wani yanayin rayuwa da karfafa hadin kan jama'a ta hanyar aiwatar da wata siyasa mai kyau, da halartar kowa da adalci da zummar warware matsalolin tattalin arziki da na jama'a. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China