Wannan ne karo na farko da ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, da hukumar kwastam ta Najeriya suka dauki nauyin gudanar da wannan kwas. Jami'an kwastam na Najeriyar 40 ne suka halarci bikin kammala karatun.
An ce, an raba kwas din gida 7, inda ake gudanar da ko wane kashi cikin watanni 7. Ana koyar da ma'aikatan kwastam din Najeriya kimanin 300 yaren Sinanci. Bayan kammala karatun, za su iya amfani da yaren wajen karbar masu bukatar amfani da Sinanci a filin jiragen saman birnin Abuja. (Zainab)