in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta damke bakin haure sama da 3,000 dake zaune a kasar ba bisa ka'ida ba
2016-10-21 10:16:05 cri
Jami'an hukumar shigi da fici ta Najeriya NIS, sun tabbatar da cewa, sun kama mutane sama da 3000 dake zaune cikin kasar ba bisa ka'ida ba a jahar Legas, cibiyar kasuwanci ta kasar.

Tun da sanyin safiya ne dai manyan motocin jami'an sama da 40 dake dauke da makamai suka kewaye wasu tashoshin mota da shaguna da otel otel, da wasu wuraren shakatawa inda baki 'yan kasashen waje ke taruwa.

A lokacin samamen, jami'an na NIS, sun yi harbe harbe a sararin sama domin ankarar da bakin hauren don shiga taitayinsu.

Mafi yawan bakin hauren da aka damke sun fito ne daga kasashen Ghana, Benin Republic, Niger, Mali, Cote d'Ivoire da Togo.

Wata majiya daga hukumar shigi da ficin ta shedawa kamfanin dillancin labaran Xinhua cewa, dalilan da suka sa hukumar daukar matakan cigaba da farautar bakin hauren shi ne, saboda wasu bayanai da ake bazawa cewa mafiya yawan bakin hauren dake cikin kasar ba bisa ka'ida ba suna da alaka da kungiyar Boko Haram.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China