in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmnan labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-10-19 20:45:41 cri
Fadar shugaban Najeriya ta fitar da wata sanarwa a daren ranar Talata wadda ke cewa, gwamnatin Muhammadu Buhari,ba za ta ci zarafin kowa ba bisa kowane irin dalili. Amma kuma ta ce, duk wanda ya taka doka, to fa doka za ta taka shi.

Gwamnatin ta kuma jaddada cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa ba, game da shirin ta na yaki da cin hanci da karbar rashawa.(Vanguard)

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci dukkan bangarori a tattaunawar da ta kai ga sakin 'yan matan Chibok 21, da su tabbatar da cewa,an saki ragowar mutanen da ke tsare a hannun mayakan na Boko Haram.

Majalisar dattawan ta kuma godewa wadanda suka shiga tsakani game da sakin 'yan matan sakandaren na Chibok guda 21. Sai dai kuma ta ce, akwai wasu mutane da dama wadanda Boko Haram suke tsare da su da ba a ba da rahotonsu ba. Ta ce kamata ya yi a fadada tattaunawar da ake yi don ganin an saki karin wadanda ake tsare da su, maimakon 'yan matan chibok kadai.(The Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China