Shugaba Buhari ya ce, a shirye ya ke ya ci gaba da tattaunawa da kungiyar muddin za ta amince ta sanya kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross(Daily Trust)
Karamin ministan albarkartun man fetur na Najeriya Ibe Kachikwu ya bayyana a yau Litinin cewa, mahukuntan kasar sun fara yin shawarwari da gwamnatin kasar Indiya kan yadda za ta fara biyan dala biliyan 15 na danyen man da ta saya daga kasar.(The Punch)
Majalisar dokokin Najeriya ta yanke shawarar ranto kudade daga bankuna wajen biyan ma'aikatanta kudadensu na albashi da alawus-alawus, sakamakon karancin kudin da ta ke fuskanta. Amma matakin bai shafi kudaden da 'yan majalisar ke bukata wajen tafiyar da harkokin majalisa, albashi, alawus-alawus da na mataimakansu ba.(The Guardian)