in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje a kalla 4000 a Najeriya
2016-09-21 11:07:28 cri

A kalla gidaje dubu 4 ne ambaliyar ruwa ta lalata a jihar Cross River dake tarayyar Najeriya, bayan an samu ruwan sama kamar da bakin kwarya masu yawan gaske a wannan kasa dake yammacin Afrika, in ji wani jami'in hukumar ba da agajin gaggawa a ranar Talata.

Haha kuma fiye da filayen noma dubu 13 wadannan ruwa suka lalata da suka shafi yankuna 7 na wannan jihar, in ji John Inaku, shugaba mai kula da harkokin hukumar ba da agajin gaggawa, a yayin wani taron manema labarai. A dunkule yankuna 46 ne wannan ambaliyar ruwa ta shafa, in ji jami'in.

Tuni gwamnatin wannan jihar dake kudancin Najeriya ta tura jiragen ruwa domin jigilar mutanen da bala'in ya shafa da kuma kai su yankunan da ruwa ba su ci ba, in ji jami'in. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China