in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar AU na nazari biyan diyya ga fararen hulan da suka jikkata a Somaliya
2016-10-11 13:15:15 cri

Tawagar kungiyar tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM) ta rawaito a ranar Litinin cewa ta fara wani aikin biyan diyya ga fararen hula da suka fuskanci barna kai tsaye a lokacin ayyukanta a cikin wannan kasa.

Daretan rukunin cigaban ayyukan siyasa a cikin rundunar ayyukan tabbatar da zaman lafiya, mista Jide Okeke, ya bayyana cewa kwamitin tarayyar Afrika na ganin cewa wannan mataki zai karfafa dangantaka da amincewa da juna tsakanin AMISOM da al'ummar Somaliya.

Wannan na cikin tsarin kokarin mu na samun karbuwa a cikin zukatan al'ummomin Somaliya, lamarin da ya kasance wani muhimmin mataki na yaki da kungiyar Al-Shebab, in ji mista Okeke a cikin wata sanarwa a birnin Mogadishu.

Wannan shiri, na farko irinsa a nahiyar Afrika, zai samar wa mutanen da ayyukan AMISOM suka rutsa da su wata diyya.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China