in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun AU sun kashe mayakan Al-Shabaab 7 a kudancin Somaliya
2016-10-06 11:51:38 cri
Rahotanni daga kasar Somaliya na cewa, tawagar kungiyar tarayyar Afirka da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya(AMISON) ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe a kalla mayakan kungiyar Al-Shabaab 7 tare da jikkata wasu 11 a yayin da mayakan kungiyar suka yi musu kwanton bauna a garin Janale da ke kudancin Somaliya a yammacin ranar Talata.

Mazauna yankin sun ce kwanson albarusai da dama sun fada a tsakiya da kuma kusa da wajen garin, lamarin da ya haddasa mutuwar 'yan kungiyar ta Al-Shabaab da dama.

Sai dai har yanzu kungiyar wadda ta shafe shekaru da dama tana fada da gwamnatin Somaliya ba ta yi wani karin haske ba.((brahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China