A wata sanarwa da kungiyar ta rabawa manema labarai a jiya Alhamis, AMISOM ta ce, wurin da dakarunta suka halaka mayakan kungiyar Al-Shabaab 7 yana nesa da yankunan da jama'a ke zaune. Haka kuma tawagar tana ba da muhimmanci sosai ga tsaro da kare rayukan fararen hula a duk lokacin da ta ke gudanar da ayyukanta.
Kafofin watsa labarai a yankin suna ikararin cewa, an kashe fararen hula biyar kana wasu da dama kuma suka jikkata a harin da dakarun na AMISOM suka kaddamar a wani yankin da ke kusa da garin Janale da ke Lower Shabelle.
Tawagar AMISOM dai tana taimakawa sojojin Somaliya ne a yakin da suke yi da mayakan Al-Shabaab, wadanda suka sha kaddamar da hare-hare a kasar.(Ibrahim)