A wata sanarwa daga ministan sadarwa na kasar Edward Omane Boamah, ya fada cewar, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan wata tattaunawa tsakanin babban kwamitin baiwa shugaban kasar shawara game da sha'anin kundin tsarin mulkin kasa, inda fadar shugaban kasar ta yi amfani da karfin ikonta wajen daukar wannan mataki.
'Yan jaridun 3 su ne: Salifu Maase, da Alistair Nelson da kuma Ako Gunn, wadanda kotun kolin kasar ta yanke musu hukuncin daurin watanni hudu a gidan kaso da kuma biya tara na kudin kasar Cedis dubu 10 kwatankwacin dalar Amurka 2,527 kowannensu.
'Yan jaridun uku, sun watsa bayanai a shirye shirye da suka gabatar ta gidajen radiyoyinsu, inda suka yi barazana game da hukuncin da kotun kolin kasar ta zartar game da soke yin amfani da katin lafiya na inshora wato NHIS a matsayin katin zabe.
Tun da farko dai kotun kolin kasar, ta zartas da hukuncin haramta yin amfani da katin na NHIS a matsayin katin shedar zama dan kasar.
Hukuncin daure 'yan jaridun, ya haifar da zazzafar mahawara a fadin kasar. Lamarin da ya sa mambobin babbar jam'iyyar kasar ta NDC suka gabatar da koke, inda suka bukaci shugaban kasar ya yi afuwa ga 'yan jaridun uku. (Ahmad Fagam)