in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Ghana ta yi watsi da kudurin bincike kan shugaban kasa game da wata kyautar mota
2016-09-02 10:00:28 cri
Majalisar dokokin kasar Ghana ta yi watsi a ranar Alhamis da wani kudurin da gungun 'yan majalisa maras rinjaye suka aje tare da kiran a gudanar da wani bincike kan shugaban kasa John Dramani Mahama bayan ya karbi wata kyautar motar daga wani hamshakin mai gina hanyoyi na kasar Burkina Faso.

Mista Mahama ya sami suka sosai bayan ya karbi wannan mota kirar Ford Expedition, da darajar kudinta ta kai dalar Amurka dubu 100, a matsayin wata kyautar daga Djibril Kanazoe, da ake tsammanin domin tankwasa shi ne.

Da yake jawabi gaban 'yan majlisar bayan sun dawo daga hutu, shugaban majalisar dokokin Ghana, Edward Doe Adjaho, ya bukaci mambobin sabuwar jam'iyyar adawa ta NPP dake cikin gungun maras rinjaye, da suka kai wannan batu gaban kwamitin hakkin dan adam da harkokin shari'a (CHRAJ).

Matakan dokar da na kundin tsarin mulki sun nuna cewa CHRAJ ita ce hukumar dake kula da batutuwan dake da nasaba da laifuffukan shugabannin jama'a, har ma da batun wannan mota kirar Ford Expedition, in ji mista Doe Adjaho.

CHRAJ ta jima da samun koke koke daban daban dake shafar wannan batu kuma ta fara gudanar da bincikenta.

Fiye da 'yan majalisa 100 na gungun maras rinjaye suka sanya hannu kan wata shawarar, da aike wa shugaban majalisa, domin bukatarsa da ya dawo da 'yan majalisar da suka tafi hutu domin a kaddamar da aiki bincike kan shugaba Mahama da kuma kyautar motar da ya karba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China