in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na hasashen zuba kusan dalar Amurka biliyan 15 a cikin tattalin arzikinta
2016-09-21 11:06:08 cri

Gwamnatin Najeriya ta bayyana a ranar Talata cewa, tana aiki kan wani shiri domin janyo da zuba wasu makudan kudi a cikin tattalin arzikinta, musammun ma kudaden waje, da yawansu ya kai adadin dalar Amurka biliyan 10 zuwa 15.

A cikin wata sanarwa a birnin Lagos, ministan kudi da fasalin kasa, Udoma Udo Udoma, ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kuma shirya wata dabarar ingiza kasafin kudi da zai taimakawa kasar fita daga koma-bayan tattalin arziki.

Rukunin kula da tattalin arziki ya yi aiki wajen bullo da wani shiri domin zuba wani babban kason kudi mai muhimmanci a cikin tattalin arzikin kasar, in ji mista Udoma.

Wadannan kudade za a samu ta hanyar sayar da kadarori, biyan kudi kafin lokaci da sabunta lasisi, jinginar kayayyaki, yin amfani da kudaden haraji da dai sauransu, domin cike gibin rashin kudade.

Ministan ya jaddada wajabcin fitar da tattalin arzikin kasar daga koma-baya, ta hanyar zuba wani tarin kudi mararen a cikin tattalin arziki.

Kasar ba ta ci nasarar fadada tattalin arzikinta ba da cimma maradunta na kasa dalilin wani rashin da'a a lokacin baya, lamarin da ya janyo wani ja –da-baya ga kasar, in ji mista Udoma tare da bayyana cewa, gwamnatin ta kafa matakai domin fadada tattalin arzikinta.

Wasu daga cikin wadannan matakai sun hada da tinkarar kalublolin dake kawo cikas ga halartar bangaren masu zaman kansu a cikin bangaren man fetur daga tushe, da kuma ci gaba da daidaita kayayyakin man fetur. Hakan zai karfafa bunkasa noma domin kare kasa daga karancin abinci, domin shigo da abinci na wakiltar matsayi na uku na bukata mafi girma na kudaden waje. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China