in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya za ta sake bude makarantar midil cikin mawuyacin hali mai sarkakiya
2016-09-20 12:52:58 cri

Wani jami'in kasar Nijeriya ya sanar a jiya Litinin 19 ga wata cewa, Nijeriya za ta sake bude makarantun midil a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar a ranar Litinin mai zuwa, bayan shekaru biyu da gwamnati ta sanar da rufe wadannan makarantu sakamakon hare haren ta'addanci na kungiya mai tsatsauran ra'ayi ta Boko Haram a wannan yanki.

Kwamishina Inuwa Kubo, mai kula da harkokin ba da ilmi a jihar Borno ya shedawa manema labaru a Maiduguri, hedkwatar jihar cewa, an gudanar da wannan shiri ne bayan da aka gyara wadannan makarantu.

An ba da labari cewa, an rufe wadannan makarantu a jihar Borno ne tun a cikin watan Maris din shekarar 2014, saboda fargabar hare haren Boko Haram, bayan kungiyar ta kai hari a wata makaranta a jihar Yobe dake makwabtaka da jihar Borno.

Matsalar ta'addanci ta dabaibaye jihar Borno cikin dogon loakci. A cikin watannin da suka gabata, gwamnatin tarayya ta tura sojojinta sau da dama zuwa wannan jihar domin yaki da ta'addanci.

Mista Kubo ya ce, an sake bude makarantun firamare tun a shekarar bara, amma ba a bude makarantun midil ba a waccan lokaci, saboda an yi amfani da wadannan makarantu wajen tsugunar da 'yan gudun hijira.

Mista Kubo ya kara da cewa, gwamnatin ta yi shirin gyara wadannan makarantu saboda 'yan gudun hijira sun lalata su.

Ban da wannan kuma, gwamnati ta yi kira da kuma kalubalantar iyayen dalibai da su kai yaransu zuwa makarantu, tare da jaddada cewa, hana dalibai shiga makarantu zai haifar da illa sosai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China