in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 30 a Syria
2016-10-04 12:40:18 cri
Rahotanni daga kasar Syria na cewa, a kalla mutane 30 ne suka mutu, kana wasu 90 kuma suka jikkata, sakamakon wani harin kunar bake da aka kaddamar a wajen wani shagalin biki na kabilar Kurdawa a lardin Hasakah da ke arewa maso gabashin kasar Syria.

Gidan talabajin da ke yankin bai yi wani karin haske ba, amma kungiyar kare hakkin bil-Adama ta kasar Syria, ta ce maharin ya tayar da bam din da ke jikinsa ne a cikin dakin da ake bikin wanda ke wani yanki a kan hanyar Hasakah zuwa birnin Qamishli, yankin da ke tsakanin wuraren duba ababan hawa biyu na dakarun Kurdawa a yankin da Kurdawa suka fi yawa.

Kungiyar da ke da matsuguni a kasar Burtaniya ta bayyana cewa, bam din ya fashe ne a lokacin da ake tsakiyar shagulgulan bikin, kuma da alamun yawan mutanen da suka mutu na iya karuwa sakamakon munanan raunukan da jama'a suka ji.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari, amma da alamun kungiyar IS ce ta kai harin, ganin yadda ta sha kaddamar da makamantan hare-haren kunar bakin wake kan dakarun Kurdawa da al'ummar Hasakah, lardin da ke karkashin ikon dakarun Kurdawa da sojojin gwamnatin Syria. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China