Wakiliyar hukumar ta UNHCR a Najeriya, Angele Dikongue-Atangana, ta sanar da wannan kididdiga a ranar Alhamis din nan a Abuja babban birnin kasar, a yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki na hukumar na shekarar 2015.
Dikongue-Atangana, ta ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafawa wadanda matsalar ta shafa, sannan ta bukaci sauran hukumomin bada tallafi na duniya da su tallafawa mutanen da matsalar ta shafa.
Ta kara da cewar, a wannan shekarar ta 2015, hukumar ta UNHCR ta samu nasarori masu yawa a Najeriyar, musamman wajen tsugunar da wadanda rikicin ya raba da matsugunan su, da kuma samar da hadin gwiwa da hukumar ECOWAS.
A cewarta, hukumar ta taimaka wajen mayar da wasu 'yan asalin jamhuriyar Kamaru su 452 zuwa gidajen su, sannan ta ce a halin yanzu, an shirya sake mayar da karin wasu mutanen kimanin 165 zuwa kasashensu wadanda ke gudun hijira a yankunan kasashen Turai da Amurka.(Ahmad Fagam)