Ministan ma'aikatar cikin gidan kasar Tayeb Belaiz ne ya tabbatar da hakan, jim kadan bayan ganawarsa da takwaransa na Nijer Massaoudou Hassoumi.
Kamfanin dillancin labaru na APS ya rawaito Mr. Belaiz na cewa za a maida 'yan gudun hijirar, musamman wadanda suka tsallaka Aljeriya ba tare da izini ba gida ne bisa bukatar hakan daga mahukuntan Nijer. Sai dai ya ce za a kiyaye dukkanin hakkokin su, tare da martaba 'yancin su yadda ya kamata.
Yanzu haka dai akwai daruruwan 'yan Nijer dake gudun hijira a kasar ta Aljeriya. Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa da daman su mata ne da kananan yara da suka tserewa halin matsi da kuma karancin abinci. (Saminu Alhassan)