Da yake magana gaban wakilai na bangaren hada hada a Johannesburg, mista Gordhan ya nuna cewa nan da karshen shekara, za mu samu cibiyar shiyya a Johannesburg, tare da kimanta wannan da wani babban aiki.
Haka kuma ya bayyana cewa manufar cibiyar shiyyar shi ne na tabo maganar zuba jari a Afrika, da bunkasa gine ginen ababen more rayuwa domin ingiza ci gaban tattalin arzikin nahiyar.
Cibiyar za ta yi koyi daga wajen manyan hukumomin kasa da kasa dake akwai yanzu kan abin da ya kamata a yi da abin da bai kamata a yi ba, in ji ministan.
Mista Pravin Gordhan ya bayyana cewa sabon bankin ci gaban zai bude wani sabon babi kan samar da kudaden gudanar da manyan ayyuka a Afrika, ta hanyar taimakawa kasashen wajen shirya manyan ayyuka, tsara manyan ayyuka masu nagarta da kuma aiwatar da manyan ayyukan har zuwa kammala su. (Maman Ada)