in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamiyyar ANC ta samu koma baya a zaben kananan hukumomi a Afrika ta kudu
2016-08-07 13:21:59 cri
Sakamakon zaben kananan hukumoni da aka samar a jiya Asabar ya nuna cewa, Jam'iyya ANC mai mulki a Afrika ta kudu ta samu matukar raguwar magoya baya.

Mafi yawancin kuri'un da aka kada a duk fadin kasar, ya nuna cewar farin jinin jam'iyyar mai mulki yayi matukar raguwa daga kashi 61.9 cikin 100 a shekarar 2011 zuwa kashi 54 cikin 100 a shekarar ta bana, yayin da jam'iyyar Democratic Alliance wato (DA) ke cigaba da samun karbuwa wacce ta samu karuwa daga kashi 23.9 cikin 100 zuwa kashi 27.1 cikin 100.

Jam'iyyar DA tana kara samun magoya baya a dukkan yankunan kasar, musamman ma wuraren da a baya jam'iyyar ta ANC keda rinjaye.

Abu mafi muhimmanci shi ne, jam'iyyar DA ta lashe mahaifar tsaohon shugaban kasar Nelson Mandela, wanda a can ne aka yankewa jam'iyyar ta ANC cibiya.

A can birnin, DA ta kasance jam'iyyar mafi girma bayan da ta lashe kashi 46.71 cikin 100 sama da kashi 40.13 data lashe a zaben shekarar 2011.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China