Sakamakon zaben na baya-bayan da aka fitar yana nuna cewa, jam'iyyar ANC ta samu kaso 54.15 cikin 100 na kuru'un da aka kada a fadin kasar, yayin da jam'iyyar Democratic Alliance (DA) take biye da ita da kaso 26.9 cikin 100.
Mai magana da yawun jam'iyyar Zizi Kodwa ya ce, wannan sakamakon ya sake nuna irin tabbacin da al'ummar kasar Afirka ta kudu suke da shi a kan jam'iyyar.
Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin zabukan na wannan karo a matsayin mafi zafi tun bayan zaben shekarar 1994. Kuma wannan shi ne karon farko a cikin tarihin kasar, da jam'iyyun siyasa 200 da 'yan takara sama da 61,000 suke neman shugabancin majalisun kananan hukumomin kasar sama da 200. (Ibrahim)