in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta dakatar da tattaunawa da Rasha game da batun tsagaita wuta a Syria
2016-10-04 11:47:11 cri
Amurka ta bayyana dakatar da tattaunawa da Rasha, game da batun tsagaita bude wuta a Syria, sakamakon abun da ta kira rashin cika alkawuran da Rashan ta dauka game da batun.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka John Kirby ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar a jiya Litinin. Sanarwa ta ce ko dai Rashan ba ta da sha'awa, ko kuma ta gaza wajen tabbatar da cewa Syria ta aiwatar da matakan da aka amince da su na tabbatar da nasarar shirin.

Mr. Kirby ya kara da cewa, matakin da Rasha da Syria ke dauka na kaiwa ababen more rayuwa a yankunan fararen hula hari, ya dakile shigar kayayyakin jin kai zuwa wuraren da ake matukar bukatar su.

Sai dai a nata bangare mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova, ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa Amurka na kokarin dora laifin dagulewar al'amura ne kawai kan Rasha, bayan kuwa ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma, ta shigar da kayan tallafi zuwa birnin Aleppo, kana ta kasa matsawa dakarun 'yan adawar kasar lamba game da shirin na tsagaita bude wuta. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China