A jiya da safe ne kwamitin sulhu na MDD ya kira taron gaggawa domin tattauna batutuwan da suka shafi munanan hare-haren da aka kai a muhimmin garin Aleppo dake arewacin kasar Syria.
An kira wannan taro ne a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka da misalin karfe 11 na safe agogon wurin. Manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura ya gabatar da rahoto kan yadda al'amura suka rincabe a garin Aleppo.Yana mai cewa, hakan ya kawo illa sosai ga aikin kai kayayyakin agaji da MDD ke gudanarwa a yankin da kuma yanayin zaman rayuwar mazauna wurin.(Lami)