Rogerio wanda a halin yanzu yake kociyan badges, tuni ya riga ya nuna sha'awarsa ga kungiyar wasan ta Brazil wacce a sau 6 tana shiga gasar rukunin kwararru na Serie A ta kasar.
Shugaban kulob din Carlos Silva, ya shedawa gidan radiyon Globo cewa, "wata rana zai zama kociyan Sao Paulo. "hakan zai yi kyau ga kungiyar. Yana da kwazo, yana da karfin hali, kuma zai sadaukar da kai ga Sao Paulo iya bakin kokarinsa. Takardun shedar kwarewarsa sun tabbatar da komai. Ya shirya zama kociya".
Da aka tambaye shi shin ko zai iya jan ragamar kungiyar wasan ta farko a kakar wasanni mai zuwa, Silva ya bada amsa cewa: "wannan abu ne a duhu, amma zai yiwu."
Sao Paulo, wadda ita ce ta 15 a rukunin Serie A a Brazil, tana da wasanni akalla 7 da suka rage mata a wannan kakar wasannin, kuma a halin yanzu tsohon kociyan ta Bordeaux kuma shugaban Monaco, Ricardo Gomes, shine ke jagorantar kungiyar wasan.
Rogerio ya yi ritaya daga aiki a karshen shekarar bara, bayan wasanni 1,250 da kungiyar wasan Sao Paulo ta buga a tsawon wa'adin aikinsa cikin kakar wasannin 24.
Bisa kwararre a bugun free-kick da kuma bugun daga kai sai mai tsaron gida, littafin tarihi na Guinness Book of Records ya ambace shi a matsayin na farko a fagen tsaron gida da tsare kwallaye wadanda yawansu ya kai kwallaye 131.(Ahmad Fagam)