Da yake bayyana kwarin gwiwar sa ga kwallon kafar kasar, Gil mai shekaru 28 da haihuwa, ya ce tun isowar sa kungiyar Shandong Luneng daga Corinthians a watan Janairu, ya sake samun gogewa da karsashi. Ya ce dukkanin wadanda suka san shi, sun san ba shi da wasa, kuma bai zo Sin a matsayin ritaya ba, ya zo ne domin ci gaba da kwazo na samun daukaka a sana'ar sa.
Augusto wanda shi ma ya baro Corinthians zuwa Beijing Guoan, cewa yayi ya zo ne domin baje basirar sa a fagen tamaula.
Tuni dai kocin kungiyar kasar Brazil Dunga, ya sanya 'yan wasan biyu cikin wadanda za su bugawa Brazil din wasannin share fagen cin kofin duniya tsakanin su da kasashen Uruguay da Paraguay.