Yayin da ya rage kwanaki 109 kacal a bude katafaren filin wasa na Maracana, IOC ta ce wannan gasar wasannin za ta samar da muhimman damammaki wajen hada kan al'ummar kasar ta Brazil ba tare da bambancin siyasa ba.
Wata sanarwar da Jami'an na IOC suka fitar ta nuna cewar ana shirye shiryen lalubo matakan da za su tabbatar da cewa rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar ba zai shafi batun shirya gasar wasannin na Olymphic ba.
A ranar Lahadin da ta gabata ne majalisar dokokin kasar Brazil ta kada kuri'ar neman goyon bayan tsige shugaba Dilma Rousseff daga mukaminta, kuma sun mika da bukatar tsige shugabar ga majalisar dattijan kasar.
Ana zargin shugaba Rousseff ne da laifukan dake da nasaba da rashawa tun bayan sake zabarta a shekarar 2014.
Daga cikin nauyin dake wuyan gwamnatin game da shirya gasar wasannin sun hada da samar da kyakkyawan tsaro, da wuraren gudanar da wasannin da tsare tsare, kuma wannan shi ne karon farko da kasar wacce ke kudancin nahiyar Amurka zata karbi bakuncin gasar wasannin na Olympic , wadda za ta gudana daga ranar 5 zuwa 21 ga watan Augusta.(Ahmad Fagam)