Neymar, mai shekaru 24 a duniya, ya sauka daga mukamin shugaban kungiyar Selecao tun a ranar Asabar data gabata, bayan da Brazil ta lallasa Jamus a bugun daga kai sai mai tsaron gida, wanda ya bata damar lashe lambar zinare a gasar wasan kwallon kafa ta wasannin Olympics da suka gudana a birnin Rio.
Tite ya fada a taron manema labaru cewa 'na fadawa Neymar cewa, ka yi murna yanzu, kuma ka shirya zama kyaftin a nan gaba'.
Neymar dai bai bayyana dalilinsa na kin amincewa da zaman kyaftin din ba, ko da yake dangantaka tsakaninsa da kafofin yada labarai na Brazil ta taka muhimmiyar rawa.
A lokacin taron manema labarai gabanin fara wasannin Olympics a sansanin bada horo na Terespolis na kasaar Brazil, Neymar ya fada cewa, tsarin gudanar da rayuwarsa zai iya shafar harkokinsa na kwallon kafa.
Dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa, ya kusa ya daina bayyana a kafofin yada labarai, kuma yana magana ne kadai idan aka tilasta shi ya aikata hakan.