An dai gayyaci Perreira dake wasa a Manchester United ne kasancewar 'iyayensa 'yan asalin kasar Brazil ne, domin ya kasance cikin jerin 'yan wasa ashirin, da za su bugawa kasar wasan sada zumunta nan da 'yan kwanaki.
Dan shekaru 19 da haihuwa, Perreira ya buga wasa ga Brazil a bara yayin gasar Panda da ta gabata a kasar Sin. Har wa yau a baya dan wasan ya taba bugawa Belgium wasa a gasar 'yan kasa da shekaru 15 da 16 da kuma 17.
Brazil dai ta kira Perreira a daidai gabar da ake nuna damuwa, game da yadda kwararrun yan wasan kasar ke ficewa su shiga kungiyoyin kasashen waje daban daban.
Sauran yan wasan da aka gayyata domin buga wasannin sada zumunta da Brazil din za ta buga karkashin koci Alexandre Gallo, sun hada da dan wasan Real Madrid Jean Carlos, da dan wasan Marseille Alef, da na Cagliari Caio Rangel.
Bisa tsarin wasannin sada zumuntar dake tafe Brazil za ta kara da Kamaru a ranar 10 ga watan Afirilun nan, sai wasan ta da Qatar a ranar 13 ga wata, da kuma na Brazil da Honduras a birnin Pasching duka dai cikin watan na Afirilun nan.
Gasar matasan 'yan kasa da shekaru 20 kuwa, za a buga ta ne daga 30 ga watan Mayu zuwa 20 ga watan Yunin bana.