Hukuma mai kula da wasan kwallon kafa ta kasar Brazil, ta ce ya kamata a ba ta izinin maye gurbin Prass mai shekaru 38 a duniya, da wani tsohon dan wasan kasar na daban.
Bisa ka'idojin wasannin Olympics, ko wace kasa na da ikon sanya 'yan wasa 3 ne kacal wadanda shekarun su suka haura 22. Kuma cikin wannan tawaga ta Brazil banda shi Prass, sauran tsoffin 'yan wasan kasar 2 su ne Neymar da Renato Augusto.
Prass din wanda yake taka leda a kulob din Palmeiras na kasar Brazil, ya ji rauni ne a hannunsa na dama yayin da yake wasa, sa'an nan ya sake fama ciwon yayin wasan sada zumunta da aka buga tsakanin Brazil da Japan a ranar Asabar da ta wuce. Sakamakon binciken da aka yi masa, ya nuna cewa zai bukaci samun hutu har tsawon wasu makwanni, hakan ne kuma ya sanya Brazil din nuna bukatar maye gurbin sa da wani dan wasan mai shekaru sama da 22 na daban.(Bello Wang)