in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NFF ta jajantawa iyalan dan wasan kulob din kwallon kafa ta 3SC
2016-10-19 15:42:07 cri
Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta aike da sakon ta'aziyya ga iyalan mai tsaron baya na kulob din kungiyar wasan kwallon kafa ta Shooting Stars Sports dake Ibadan, Izu Joseph, wanda ya rasu a ranar Lahadi, sakamakon harsashin da ya same shi, bayan da dakarun tsaron kasar suka yi wani harbi da bindiga.

Shugaban hukumar NFF Amaju Pinnick, ya nuna damuwa matuka, bayan da ya samu labarin rasuwar dan wasan, nan take ya kira mahaifin dan wasan kwallon kafan ta wayar hannu domin jajanta masa game da rasuwar Joseph.

Pinnick ya ce, ya kadu matuka game da abinda ya faru. Wannan abu da ya faru kwatsam ya ta da hankalin 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya, kasancewar mako guda ke nan da aka kammala bikin murnar samun nasara a wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya. Ya ce wannan abu yana da zafi matuka.

Ya kara da cewa, yana rokon dukkannin 'yan wasan kwallon kafar kungiyarsa da su dinga yin taka tsantsan game da irin wuraraen da suke zaune da irin mutanen da suke tare da su a koda yaushe, saboda su kadara ce mai tsada. Ya ce, karshen al'amari dai dukkan mutane dole ne za su mutu, amma ba ya fatan yin hasarar wani dan wasa irin yadda aka rasa Izu Joseph.

Bugu da kari, mahaifin marigayin ya ce, dole ne a yi adalci game da musabbabin da ya yi sanadiyyar mutuwar dansa.

Ya ce dansa ya dawo gida ne saboda hutu, kuma kai tsaye ya wuce zuwa garinsa na asali Okaki, dake karamar hukumar Mahuda, a jahar Bayelsa; kwatsam sai ya ji labarin an harbe dansa, duk da cewar ya nuna musu katinsa na aiki da kungiyar wasa ta Shooting Stars Sports ta Ibadan.

Ya kara da cewa, yana bukatar a yi adalci game da mutuwar dansa wanda aka hallaka ba tare da an gudanar da bincike ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China