161020-mikel-iheanacho-da-musa-sun-shiga-jerin-yan-takarar-lambar-yabo-ta-caf-bello.m4a
|
A cikin jerin wadanda ke wannan takara dai akwai Pierre-Emerick Aubameyang, da Andre Ayew, da Victor Wanyama, da Riyad Mahrez, da Samuel Eto'o, da kuma Eric Bailly.
A ajin 'yan wasan da ke wasa a nahiyar ta Afirka kadai, akwai dan wasan Enyimba wanda ya fi kowa zura kwallo a raga Mfon Udoh, da kuma Chisom Chikatara, wanda yanzu haka ke taka leda a Wydad Athletic Club na kasar Morocco, wadanda su ma za su yi takara da wasu 'yan wasan su 23 dake wasa a nahiyar.
Iheanacho, ya samu damar shiga wannan takara ne sakamakon irin rawar da ya taka a kungiyar Manchester City. Dan wasan mai shekaru 20 a duniya, tuni ya zura kwallaye 4 a wasanni hudu da ya bugawa Super Eagles din a bana.
Shi kuwa Mikel Obi, wanda shi ne kyaftin din 'yan wasan Najeriya da suka samu lambar tagulla a gasar kwallon kafar Olympics da aka kammala a baya bayan nan, ya samu wannan dama ne sakamakon irin rawar da kungiyar sa ta taka karkashin jagorancin sa a gasar ta birnin Rio.
Yayin da shi kuma Musa ya nuna hazaka matuka a kungiyar kwallon kafar CSKA ta Moscow, kafin ya koma kungiyar Leicester City wadda ta lashe kofin gasar firimiyar da ta gabata.
A bangaren 'yan wasa dake taka leda a nahiyar Afirka kuwa, dan wasan Enyimba Udoh, ya zura kwallaye 9 a raga, a wasannin da ya bugawa kungiyar sa, kuma muddin Bassem Morsy na Zamalek bai kara kwallaye 6 a raga cikin wasanni biyu da kungiyar sa za ta buga da Mamelodi Sundowns ba, Udoh ne zai zamo dan wasa mafi yawan kwallaye a tsakanin kulaflikan nahiyar dake buga gasar firimiya.
Chikatara kuwa ya samu gurbin takarar sa ne a gasar CHAN da aka buga a kasar Rwanda. Tsohon dan wasan Abia Warriors ya ci kwallaye 4, ciki hadda wadanda Najeriya ta tashi 4 da 1 da janhuriyar Nijar, inda ya shiga sahun 'yan wasa mafiya cin kwallaye tare da Elia Meschak na janhuriyar dimokaradiyyar Congo, da kuma Ahmed Akaichi na kasar Tunisia.
Ana sa ran dai hukumar ta CAF za ta rage yawan 'yan takarar wannan lamba ta yabo kafin karshen wannan shekara. Sa'an nan a gabatar da bikin bada lambar a birnin Abuja a ranar 5 ga watan Janairun shekara mai zuwa.(Saminu Alhassan)