in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Man City ta yi rashin nasara yayin da Arsenal ta doke Burnley
2016-10-05 13:59:44 cri
Kungiyar kwallon kafar Ingila wato Tottenham Spurs ta dakatar da burin kocin Manchester City Pep Guardiola, na ci gaba da lashe wasannin firimiya ba tare da wata matsala ba, inda kungiyoyin biyu suka tashi wasan su na ranar Lahadi Tuttenham na da kwallo 2 Manchester City na nema.

Kafin wannan wasan dai Man city ta lashe wasanni 6 a jere da ta buga, da kuma wannin 10 cikin 11 da ta buga karkashin jagorancin Guardiola. Sai dai wasan na karshen mako ya sauya wannan matsayi, bayan da Spurs din ta daga sama zuwa matsayi na biyu a kan teburin firimiyar, kana ta zama kungiyar da kawo yanzu ba a samu nasara a kan ta ba a gasar.

Tun fara wasan dai Spurs ke kan gaba wajen kaddamar da hare hare kafin Aleksandar Kolarov ya karasa sanya kwallon da Danny Rose ya buga cikin zaren kungiyar ta Man city. Sai kuma kwallon Dele Alli mintuna 8 kafin tafiya hutun rabin lokaci. Yanzu haka dai maki daya ne tak ya raba Man city dake saman teburin da Tottenham Spurs wadda ke matsayi na biyu.

A nata bangare kuwa kungiyar Arsenal nasara ta samu kan Burnley da ci daya da nema, ta hannu dan wasan ta Laurent Koscielny, a wasan da kungiyoyin biyu suka buga a Lahadin karshen mako.

Ita kuwa Manchester United tashi ta yi kunnen doki daya da daya tare da Stoke city, wanda hakan ya bata maki daya tak da ya raba ta da kasancewa a karshen teburin gasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China