Sai dai bisa shawarar da Infantino ya gabatar, kungiyoyi 16 daga wadanda za a kara zasu buga wasa daya daya ne na fidda gwanayen gasar, yayin da sauran kungiyoyin 32 za su ci gaba da buga gasar kamar yadda ake yi a baya.
Infantino, ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudana a jami'ar Arboleda, yana mai cewa za a yanke hukuncin karshe game da wannnan batu, yayin taron kwamitin zartaswar hukumar cikin watan Janairun shekara mai zuwa.
Ya ce burin hukumar FIFA shi ne ta gina harkar kwallon kafa a dukkanin fadin duniya, ta yadda za ta wuce batun gasa kadai, wato ta zamo harkar cudanya tsakanin al'ummar duniya.
An dai zabi Infantino a matsayin shugaban hukumar FIFA ne a ranar 26 ga watan Fabarairu, inda ya maye gurbin Sepp Blatter, wanda aka dakatar daga shiga harkokin wasanni na tsawo shekaru 6.