in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gernot Rohr ya isa Najeriya gabanin wasan Super Eagles da Zambia
2016-10-05 14:01:55 cri
Sabon mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafar Najeriya Gernot Rohr tare da 'yan tawagar sa, sun sauka a Abuja fadar mulkin Najeriyar gabanin wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya dake tafe a shekarar 2018 a Rasha, inda Najeriyar za ta buga wasan ta na gaba da kasar Zambia. Rohr dan asalin kasar Faransa, ya isa Abuja tare da mataimakin sa Jean Luc Royer.

A daya bangaren kuma kyaftin din Super Eagles din Mikel John Obi ya karyata jita jitar da ake yadawa cewa ya ji rauni. Obi ya ce ana cikin koshin lafiya, zai kuma buga wasan da kungiyar sa za ta buga da kungiyar Chipolopolo a filin wasa na Levy Nwanawasa dake kasar Zambia a ranar Lahadi mai zuwa.

Yanzu haka dai ana sa ran 'yan wasan Super Eagles za su ci gaba da atisaye safe da yammaci, kafin su tashi zuwa Ndola a ranar Juma'a.

Kungiyoyin biyu za su kece reni ne a wasan na ranar Lahadi da misalin karfe 2:30 na rana, agogon kasar ta Zambia, wato karfe 1:30 agogon Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China