in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Atletico tana kan gaba a teburin gasar La Liga
2016-10-05 13:58:49 cri
Kulob din Atletico Madrid ya dare matsayi na farko a teburin gasar fitattun kuloflikan kwallo kafan kasar Spaniya a ranar Lahadi, bayan da ya lashe Valencia, haka kuma a nasu bangaren, Real Madrid da FC Barcelona sun hadu da rashin nasara a wasannin da suka buga na baya bayan nan.

A wasan da aka buga a ranar Lahadi, Diego Alves, mai tsaron gidan kungiyar Valencia, ya kara kwallaye 2 cikin bajintar da ya kafa ta tare kwallon daga kai sai mai tsaron gida, inda a yanzu kwallayen 'penalties' da ya tare tun bayan da ya fara tsaron gida a kasar Spain suka kai 19.

Sai dai kwarewarsa a fannin tare kwallo ba ta hana Antoine Griezmann na Atlentico Madrid jefa masa kwallo a raga ba, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan da suka buga, kafin kuma Kevin Gameiro ya karawa Atlentico din kwallo ta biyu. Matakin da ya sanya kungiyar ta Atlentico doke Valencia da ci 2 da ba ko daya.

A na ta bangare, Real Madrid ta yi chanjaras mai ban mamaki a gida da kulob mafi kankanta a tsarin gasar Primera Liga, wato Eibar. Sai dai idan an lura da yanayin da Real Madrid yake ciki, za a ga cewa sakamakon ba wani abun mamaki ba ne, ganin yadda Luka Modric da Casimiro ba su halarci wasan ba, kana shi ma James Rodriguez bai buga wasan ba sakamakon rauni da ya samu yayin atisayen kungiyar.

A wasan da aka buga a ranar Lahadi, 'yan wasan Madrid sun yi kura-kurai da yawa a kokarinsu na tsaron gida, kafin Fran Rico ya samu damar jefa kwallon farko a ragar Madrid din, 'yan mintuna 6 kacal bayan take wasan, kwallon da ya zama ta farko da kungiyar Eibar ta zura a ragar Real Madrid.

Daga bisani Gareth Bale ya farkewa Madrid din kwallon da aka zura musu mintuna 18 da fara wasan, sai dai 'yan wasan kungiyar ba su kara cin wata kwallo ba har aka tashi, kuma a daya bangaren Eibar ta ci gaba da mamaye wasan tare da nuna fasahohin 'yan wasan ta, duk da cewa Madrid din na sahun gaba a gasar ta La Liga kana ta samu nasarar lashe wasannin ta 4 a jere.

A nasa bangaren, kulaf din Barcelona ya kwashi rashin nasara ne a hannu Celta Vigo da ci 4 da 3 a filin wasa na Balaidos, lamarin da ya ragewa Barcelona damar darewa matsayi na farko a teburin gasar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China